23 Oktoba 2021 - 18:02
Aljeriya Ta Kauracewa Tattaunawar Kwamitin Tsaro Kan Batun Yankin Saharawi

Kasar Aljeriya, ta sanar da kauracewa zaman tattaunawar kwamitin tsaron MDD kan batun warware rikicin yankin Saharawi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Da yake sanar da hakan wakilin musamman na Aljeriya kan batun yankin yammacin sahara da kasashen larabawan Magreb, Amar Belani, ya ce wannan tattaunawar wacce ba za ta haifar da da mai ido ba.

Tattaunawar ta kwamitin tsaro ta da kasar Morocco, da masu fafatukar a ware na ‘yan Sahrawi na Polisario, da kuma kasashen Aljeriya, sai kuma Mauritaniya a matsayin mai sa ido.

Kasashen Aljeriya da Morocco dai sun jima suna takkada kan yankin na Saharawi wanda Spaniya ta yi wa mulkin mallaka.

A karshen watan Oktoban nan ne, ake sa ran kwamitin tsaron MDD, zai amince da wani sabon kudiri kan yakin na Saharawi da kuma batun tawagar MDD a yankin ta Minurso, kan shirya zaben raba gardama a yankin na Saharawi.

342/